Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Khatib Zade ya fadi hakan ne a jiya talata jim kadan bayan isarsa kasar Pakistan domin halartar taron ministocin harkokin waje na kungiyar hadin kan kasashen muslmi ta duniya OIC ,
Yace Iran ta yi amanna da hadin kai yin aiki tare da kuma riko da ginshikan al’amuran daya shafi duniyar musulmi akan nuna son kai da kare manufofi na siyasa na kashin kai da kuma bangare daya.
Da yake ishara game da batun sake kyautata dagantaka tsakanin Iran da saudiya kuwa ya bayyana fatansa na ganin alummar yankin sun amfana da kyautatuwar danganta tsakanin kasashen biyu
A jiya ne aka bude taron ministocin harkokin wajen kasashen musulmi karo na 48 a birnin Islamabad na kasar Pakistan.
342/